Wasu dalibai mata biyu na Jami’ar Tarayya Gusau, da ke Jihar Zamfara, da aka yi garkuwa da su a gidan kwanan su da ke kauyen Sabon Gida a karamar Hukumar Bungudu, sun samu ‘yanci.
Kungiyar dalibai ta jihar Zamfara (ZAMSSA) reshen jami’ar tarayya ta Gusau ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na kungiyar, Kwamared Umar Abubakar.
Kungiyar ba ta bayyana ko an biya kudin fansa ko kuma a’a ba kafin daliban mata da aka yi garkuwa da su na Sashen Microbiology na Jami’ar su sami ‘yancinsu a ranar Juma’a.
Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa, daliban mata biyu da aka yi garkuwa da su sun koma ga iyalansu bayan kwashe kwanaki 12 a hannunsu.
“Muna matukar farin ciki da samun ‘yancinmu kuma muna godiya ga mahukuntan makarantar da iyayenmu da suka shiga cikin mawuyacin hali na sace mu da zafi da damuwa mara misaltuwa”, in ji daliban.
Sanarwar ta bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da kamawa tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin da kuma daukar nauyin wannan aika-aika, komai tsawon lokaci.


