Daliban Najeriya da ke makale a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, sun roki gwamnatin tarayya da ta taimaka musu wajen kwashe su.
Daliban dai na rayuwa cikin fargaba yayin da wasu mazauna garin suka tsere, sakamakon fadan da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 300, galibi fararen hula.
Rundunar Rapid Support Forces (RSF) ta ce ba za ta zauna don tattaunawa da sojojin Sudan don tsagaita bude wuta ba gabanin sallar Idi a karshen mako.
Yakin ya tilasta wa jirgin shugaban kasa Muhammadu Buhari daukar dogon zango yayin da ya dawo kasar daga Saudiyya.
Wata sanarwa da kungiyar daliban Najeriya ta Sudan (NANSS) ta fitar ta bukaci gwamnati da ta dauki matakin gaggawa.
Sun ce a halin yanzu a Khartoum ” harbe-harbe na yau da kullun, fashewa da hare-haren jiragen sama sun mamaye kewayenta da kewaye.”
Daliban sun bayyana cewa ba su samu damar samun bukatu na yau da kullun ba kuma suna fuskantar barazana mai hatsari tun makon da ya gabata.
Sanarwar ta kara da cewa, “Muna nan, muna rubutawa, muna rokon gwamnatin kasar da ta aiko da gaggawar kwashe daliban da suka makale a tsakiyar yakin,” in ji sanarwar.


