Kungiyar dalibai ta kasa (NANS), ta bukaci dalibai da matasa da su farka daga barcin da suke yi na siyasa, su kuma shirya don zaben shugabanni masu ra’ayin matasa a zaben 2023 mai zuwa.
NANS ta kuma yi kira ga daukacin matasa da su samu katin zabe na dindindin (PVCs), domin sabuwar dokar zabe ta tabbatar da cewa, dole ne a kirga kuri’u saboda an yi amfani da damar yin magudin zabe zuwa ga mafi karanci.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis a Enugu ta hannun kodinetan NANS shiyyar (Kudu maso Gabas), Mista Moses Ibeabuchi, mai take: “Budediyar Wasika ga Matasa da Dalibai na Najeriya”.
Ibeabuchi ya ce, jimlar ‘yancin kada kuri’a na dalibai da matasa ta hanyar PVC ya kasance mai karfi da hakkin da suke da shi a kudurin su na sauya kasar nan gaba daya.
Ya kara da cewa daliban Najeriya sun shafe watanni uku suna gida suna kirga yajin aikin ASUU.
Shugaban NANS ya lura cewa shugabannin siyasa sun damu ne kawai game da sha’awarsu ta siyasa a zabe mai zuwa; kuma babu wanda ke sha’awar makomar ‘yan Najeriya a cikin tsararraki masu zuwa, yana mai cewa: “Wannan ita ce gaskiyar mu, abin bakin ciki da wanda ba a iya misaltawa”.