Mahukunta sun ce adadin daliban da suka mutu yayin rushewar ginin wata makaranta ya kai 22, sannan fiye da dari da talatin suka jikkata.
Lamarin ya faru ne a wata makarantar mai hawa biyu da ake kira Saints Academy da ke Jos, a jihar Filato jiya Juma’a, lokacin da dalibai ke tsaka da karatu, kana wasu daga cikinsu ke rubuta jarabawa.
Wakilin BBC ya ce tunda farko iyaye da dama da ke cikin matuƙar kaɗuwa sun ga yadda aka riƙa ciro gawarwakin ƴaƴansu daga cikin ɓaraguzai, yayin da masu aikin ceto suka riƙa amfani da hannayensu wajen tono ɓurɓushin ginin kankaren domin kaiwa ga yaran da ya danne,
Kawo yanzu dai ba a san musabbabin rugujewar ginin ba, sai dai gwamnatin jihar ta ɗora alhakin lamarin a kan rashin ingancin ginin da aka yi a kusa da wata madatsar ruwa da ke gaɓar kogi.


