Wani dalibi ɗan shekara 17 a makarantar Offa Grammar dake karamar hukumar Offa a jihar Kwara mai suna Adegoke Adeyemi ya kashe kansa sakamakon rashin cin jarabawar karin aji daga SS1 zuwa SS2.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, a wata sanarwa da ya fitar a Ilorin a daren ranar Laraba, ya ce, an bukaci ɗalibin da ya sake karatun ajin, amma ya ji kunya kuma ya kashe kansa.
An yi imanin cewa, ya rataye kansa ne sakamakon gaza cin jarabawar ci gaba da daga SS1 zuwa SS 2, wanda hakan ya sa ya zama dole ya rataye kansa.
Tawagar ‘yan sanda daga hedikwatar ‘yan sanda ta ofishin Offa, da misalin karfe 15.34 ne suka kwashe gawar dalibin daga wata bishiya a bayan Otal din Ariya Garden, Offa. In ji Daily Nigerian.
An kai gawar zuwa babban asibitin Offa domin a tantance gawarwakin, yayin da aka fara bincike kan lamarin.
A halin da ake ciki kuma, rundunar ‘yan sanda, ta ce rundunar ta samu nasarar cafke wani fitaccen dan kungiyar asiri a cikin jerin sunayen da ake nema ruwa a jallo na kungiyar masu yaki da ‘yan daba a ACE Supermarket, Unity Road, a lokacin da ta kama dan ta’addan mai suna Monday Ojoagbu.
Kakakin ya ce, ‘yan sanda sun kama shugaban ne a babban kanti inda aka gano su da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata.
Ya kara da cewa: “A kokarin kamo wanda ake zargin, tare da kaucewa yin barna a cikin aikin kama shi, abu ne mai wahala a lokaci guda a kama sauran ‘yan kungiyarsa da suka tsere ta hanyar amfani da kwastomomin babban kanti a matsayin garkuwa.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. An samu nasarar kwato bindiga guda daya na cikin gida da harsashi masu rai guda biyu daga hannun wanda ake zargin.”


