Wasu fusatattun mutane sun kashe wani da ake zargin dan fashi da makami ne da har yanzu ba a tantance ba, a lokacin da suke yunkurin yi wa wani mazaunin Olugboso fashi a unguwar Agege a jihar Legas.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a makon jiya.
An tattaro cewa wanda ake zargin wanda ya kutsa cikin wani gida mai suna Victor, ya shiga hannun ‘yan kungiyar ne da wata bindigar wasa wadda yake amfani da ita wajen tsoratar da wadanda abin ya shafa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, hukumar ta ce an ajiye gawar wanda ake zargin a dakin ajiyar gawa, yayin da Victor, wanda ya yi fada da wanda ake zargin, yana karbar magani a asibiti.


 

 
 