fidelitybank

Ɓarawo ya rasu ya na ƙoƙarin yin sata a ƙarƙashin mota

Date:

 

 

An tsinci gawar wani mutum da a ke zargin ɓarawo ne a ƙarƙashin wata mota a Ago Egun, bodar Idiroko da ke Jihar Ogun.

Jaridar Tribune ta rawaito cewa a na zargin ɓarawon ya yi yunƙurin kwance wasu muhimman abubuwa a jikin motar, amma sai jak ɗin ɗaga mota da ya yi amfani da shi wajen ɗaga motar ya goce bayan ya riga ya shiga ƙarƙashin ta, inda motar ta faɗo masa.

Soji Gonzalo, Kwamandan rundunar bijilante ta jihar, ya baiyana cewa su na cikin sintiri ne sai su ka ga gawar mutum a ƙarƙashin wata tsohuwar mota a wani garejin gyaran mota.

Ya ƙara da cewa sun gano gawar mutumin ne da misalin ƙarfe 6 na yamma a Ago Egun ranar Alhamis.

Gonazlo ya baiyana cewa binciken su na farko ya nuna cewa motar ta daɗe a garejin wanda sama da shekara biyu ba amfani da shi kuma duk yi kurin samun wanda ya ke da filin garejin ya ci tura.

“A yanzu dai mun ɗauke gawar da kuma jak da mu ka samu mai launin ja da kuma almakashi da sauran sifanu za mu kai wa ofishin ƴan sanda na Idiroko domin faɗaɗa bincike,” in ji Gonzalo.

 

tribune news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp