Ɓangaren jam’iyyar APC da gwamna Kano ke jagoranta a Kano, ya ce, a shirye yake ya yi tafiya da ɓangaren Senata Ibrahim Shekarau ba tare da nuna wani bambanci ba.
Hakan ya biyo bayan matakin kotun daukaka kara a Abuja da ta tabbatar wa bangaren Gandujen shugabancin jam’iyya.
Uwar jam’iyyar APC ta kasa kuma ba ta yi jinkiri ba, wajen bai wa bangaren shaidar shugabanci a jihar Kano.
Bangaren Senata Shekarau dai ya nuna rashin jin dadinsa game da wannan matakin da kuma wadansu kalamai da suke ce, gwamna Ganduje ya yi, wadanda suke zargin cewa babu dattako a ciki.
Sai dai Honarabul Kabiru Alhassan Rurum, dan majalisar wakilai kuma daya daga cikin jiga-jigan ɓangaren gwamna Ganduje ya shaidawa BBC cewa, su fatan su shi ne ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau, ya manta da komai su koma tamkar yadda suke a baya.