Ƴar wasan Olympics ta Uganda Rebecca Cheptegei ta mutu bayan da tsohon saurayinta ya zuba mata fetur ya ƙona ta, kamar yadda jami’ai suka bayyana.
‘Yar gudun fanfalaƙin mai shekara 33, wadda ta fafata a birnin Paris, ta samu ƙone-ƙone sosai a duk jikinta.
Hukumomi a arewa maso yammacin Kenya, inda Cheptegei ke zaune sun ce lamarin ya faru ne bayan da ta koma gida daga coci.
Hukumomin ƙasar sun yi imanin cewa Rebecca da tsohon saurayinta na ta taƙaddama kan wasu filaye.
Ƴar wasan ta rasu sakamakon ƙunan, yayin da tsohon saurayin nata shi ma ya samu ɗan ƙuna kuma yana karɓar kulawa a asibiti.
Cheptegei ta taɓa lashe lambar yabo ta zinare a Gasar gudu ta 2022.
Lamarin na zuwa ne shekara biyu bayan kisan wasu ‘yan wasan ƙasar biyu waɗanda ke yankin gabashin Afirka, Agnes Tirop da Damaris Mutua, tare da bayyana samarinsu a matsayin waɗanda ake zargi da kashe su.
Mutuwar tata na nuna yadda ake ƙara nuna damuwa game da cin zarafin mata ‘yan wasa a Kenya.