Wata ‘yar Najeriya mai suna Adedamilola Adeparusi, ta cika burinta wajen kammala girkin sa’o’i 120, a wani yunƙuri na karya tarihin da wata ‘yan ƙasar ta kafa na shafe sa’o’i masu yawa tana girki ba tare da hutawa ba.
A ranar Talata ne Kundin Adana Tarihi na Duniya (Guinness World Records) ya tabbatar da Hilda Baci a matsayin wadda ta fi kowa daɗewa tana girki ba tare da hutawa ba.
Hilda ta shafe sa’o’i 100 tana girki inda take hutun minti biyar cikin kowacce sa’a ɗaya.
To sai dai Kundin Adana Tarihin na Duniya ya ce sa’o’i 93 da minti 11 ne Hilda Baci ta kwashe tana girkin ba 100 kamar yadda ta yi iƙirari tun da farko.
Mutanen da suka taru domin shaida girkin Misis Adeparusi da aka fi sani da Dammy ‘yar asalin jihar Ekiti, sun barke ta sowa a daidai lokacin da ta kammala girkin nata.
A ranar Laraba ne ta wallafa a shafinta na Twitter cewa ”Na kammala girkin sa’o’i 120. Ina miƙa saƙon godiya a gare ku bisa taimakon da kuka nuna min ta fuskar ƙarfafa gwiwwa da kuɗi da shaida yadda na gudanar da aikin da addu’o’inku. in ba don taimakon da kuka ba ni ba, da hakan bai kasance ba”.
Kawo yanzu dai Kundin Adana Tarihin na Duniya bai yanke hukunci kan duba yunƙurin kafa tarihin da misis Dammy ta yi ba.
To amma kasancewar Hilda Baci ba ta daɗe da kafa wannan tarihi ba, mutane a shafukan sada zumunta na ta sukar yunkurin Dammy, inda wasu ke kallon yunƙurin nata a matsayin ƙoƙarin ƙwace fice ko tarihin da Hilda ta yi a fannin


