fidelitybank

Ƴansanda sun kama Mutane fiye da dubu 30 tare da ƙwato makamai a shekara guda

Date:

Babban sufeto janar na ƴansanda, Kayode Adeolu Egbetokun ya ce jami’an rundunar sun kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban har mutum 30,313, sannan sun ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar 2024.

Shugaban ƴansandan ya bayyana haka ne a taron ganawa manema labarai a ranar Talata, 24 ga watan Disamba a Abuja.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce sun bayyana nasarar da suka samu ne domin nuna irin shirin fuskantar baɗi da suke yi.

Shugaban ƴansandan ya yaba da ƙokarin jami’ansa da sadaukarwar da suka yi a shekarar, inda ya ƙara da cewa an samu nasarar ce tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, inda ya ƙara da cewa ana buƙatar hakan domin tabbatar da tsaro mai inganci.

“Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar daƙile masu aikata laifuka, inda ta samu nasarar kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban guda 30,313 da ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250, sannan mun ceci waɗanda aka yi garkuwa da su guda 1,581.”

Ya kuma yi kira ga hafsoshin rundunar su riƙa amfani da kimiyyar zamani domin aikinsu ya ƙara nagarta.

naija hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...

Isra’ila ta gano gawar ƴan ƙasarta

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano gawar ''yan...

Ma’aikatan wutar lantarki a Abuja sun fusata

Ma'aikatar kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja Electricity Distribution...

Ƴan Najeriya 147 da suka maƙale a Nijar sun dawo gida

Gwamnatin Najeriya ta tarɓi 'yan ƙasar 147 aka kwaso...
X whatsapp