Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana 19 da ake zargin an yi safararsu zuwa Najeriya.
Cikin wata sanarwa da rundunar ƴansandan jihar Oyo ta fitar, ta ce an kama mutanen ne a Ibadan, babban birnin jihar.
Ƴansandan sun ce sun kuɓutar da mutanen ne bayan samun bayanan sirri kan ayyukan waɗanda ake zargi da safarar mutane a wasu gine-ginen birnin.
Kakakin ƴansandan, Adewale Osifeso ya ce matasan da suka haɗa da maza 14, mata biyar, an yaudare su zuwa Najeriya da nufin samar musu ayyuka.
Rahotonni na cewa tuni aka miƙa matasan hannun hukumar shige da ficen ƙasar domin faɗaɗa bincike.
Ana kuma sa ran mayar da su Ghana da zarar an kammala binciken.