Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, ta tabbatar da kwato wata mota kirar Mercedes Benz GLB 250 wadda kuɗinta yakai naira miliyan 55 da wani mai son saye ya sace.
Wani dillalin mota mai suna Mohammed Manga ya zargi Henry, wanda ya yi kama da abokin ciniki, ya tsere da motar yayin da yake gwada ta a babban birnin tarayya Abuja.
Mohammed ya ce daya daga cikin abokansa wanda kuma dillalin mota ne ya kai motar Mercedes Benz wurin wani mai son saye (Henry) domin siyar da ita, amma matsala ta fara ne lokacin da Henry ya roki ya gwada motar bayan an daidaita farashin a kan Naira miliyan 55.
Sai dai ya zarce da motar kuma tun daga lokacin ba a same shi ba.
Daga baya rundunar FCT ta bayyana Henry ya shiga hannu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Josephine Adeh ta shaidawa manema labarai a daren Laraba cewa, an gano motar a jihar Delta.
A cewarta, kwato motar da rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta yi, “alama ne na hadin gwiwar ‘yan sanda a fadin ƙasa”.
“Hukumar ƴansandan FCT tun farko ta fara gudanar da bincike na gaskiya game da lamarin, kuma ta sanar da wasu Dokokin da suka kai ga gano motar,” inji ta.


