Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya yi wa ‘yan ƙasa jawabi, inda a ciki ya bayyana abubuwa da dama kamar taron ƙasa da ya ce zai shirya domin matasa “da zimmar inganta makomar ƙasa”.
A cewarsa: “Jagorancinmu a yanzu yana ɗamfare da tunanin makomar da muke son gadar wa jikokinmu, inda muke sane da ba zai yiwu a gina rayuwarsu ta gaba ba ba tare da su a aikin ba. “A saboda haka ne nake farin cikin sanar da ku wani Taron Ƙasa Na Matasa.”
Ya ƙara da cewa taron wata dama ce da za a tattauna matsaloli da damarmaki da ke gaban matasan da su ne kusan kashi 60 na al’ummar ƙasa.
“Taron zai taɓo muhimman batutuwa kuma ya bai wa matasanmu damar saka hannu wajen gina ƙasa. Taron na kwana 30 zai haɗa kan matasa na ƙasa baki ɗaya domin lalubo mafita game da batutuwa kamar ilimi, da aikin yi, da ƙirƙira, da tsaro, da kuma adalci.”


