fidelitybank

Ƴanbindiga sun sace fasinjoji sama da asirin a jihar Neja

Date:

An sace fasinjoji sama da ashirin a wasu motoci biyar a kan hanyar Mariga zuwa Kontagora da ke jihar Naija.

Shugaban majalisar dokokin jihar wanda kuma shi ne wakilin mazaɓar Mariga inda lamarin ya faru, Abdulmalik Sarkin-Daji ya tabbatar da labarin ga manema labarai, kamar yadda jaridar Dailt Trust ta ruwaito.

Ya ce ɓarayin sun datse hanyar ne ta Mariga zuwa Kontagora a shekaran jiya Alhamis a daidai titin Babbar-Lamba da Beri inda suka yi awon-gaba da fasinjojin.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan yadda sojojin Najerya suka musanta labarin da ke cewa ɓarayin daji sun kama sansanin horonsu a yankin ƙaramar hukumar Kontagora, yankin da ya kai har Mariga.

Abdlmalik ya ce, iyalan waɗanda aka sace a baya suna kai wa ɓarayin dajin kuɗin fansa sau da dama a cikin dajin, wanda ya ce ɓangare ne na sansanin atisayen sojin.

Ya ce wasu daga cikin waɗanda ɓarayin ke garkuwa da su sun gaya wa ‘yan uwansu cewqa an tsare su ne dajin da ba shi da nisa da barikin soji na Kontagora.

Shugaban ya ce su ma waɗanda aka sace ranar Alahamis an kai su dajin ne, inda ya yi kira ga hukumomin sojin na Najeriya da su nemi bayanai na gaskiya su je su kawar da waɗannan ɓarayin daji.

Jariadr ta ce, kakakin rundunar ‘yansandan jihar ta Naija Wasiu Abiodun ya ce zai samo cikakken bayanin satar mutanen kafin ya yi magana amma kuma ba a ji shi ba.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp