fidelitybank

Ƴan wasan Yobe Desert sun yi hatsarin a mota

Date:

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Yobe Desert Stars sun gamu da hatsarin mota a ranar Alhamis yayin da suke tafiya Birnin Kebbi domin buga gasar lig.

A cewar wani rahoto daga kungiyar ‘yan jarida ta Desert Stars, hatsarin da ya afku a Sokoto, ya yi sanadin kananan raunuka ga jami’ai uku da wasu ‘yan wasa, wadanda aka yi musu jinya a wani asibiti da ke yankin.

Kungiyar ta yi kira ga magoya bayanta da masu sha’awar kwallon kafa a Damaturu da su yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata.

“Muna kira ga magoya bayanmu da dukkan masoya kwallon kafa da su kwantar da hankalinsu tare da yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata a hadarin,” in ji kulob din.

Hadarin dai ya hada da wata babbar motar safa da ke jigilar ‘yan wasan da jami’ansu, saboda bas din kungiyar ba ta cikin tsari.

Kokarin jin ta bakin jami’ai a wurin da kuma Damaturu domin jin ta bakinsu ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

daily post news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp