Kocin Super Eagles, Jose Peseiro, ya bayyana cewa, ‘yan wasansa sun matsa masa ya amince da rage masa albashi daga hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF.
Kocin dan kasar Portugal din ya amince a rage masa albashi a bazara domin ya ci gaba da jagorantar Super Eagles.
Kocin mai shekaru 63, zai jagoranci ‘yan Afirka ta Yamma zuwa gasar cin kofin Afirka na 2023 a Cote d’Ivoire a watan Janairu.
Tsohon dan wasan Saudiyya da Venezuela ya yi ikirarin cewa ‘yan wasansa sun roke shi da ya zauna domin su samu nasara a gasar.
“‘Yan wasan sun tura ni in zauna saboda sun yi imanin cewa za mu iya yin nasara (AFCON),” kamar yadda ya shaida wa Sky Sports.
“Za mu iya cin nasara. ‘Yan wasan sun san shi. Suna zuwa da kuzari iri daya, imani iri daya, don yin yaki da Super Eagles.”
Super Eagles dai sun kasance a rukunin A da mai masaukin baki Cote d’Ivoire da Equatorial Guinea da kuma Guinea-Bissau.


