Firaministan Syria, Mohammed Ghazi al-Jalali ya ce ƙasar za ta shirya sahihi kum ingantaccen zaɓe cikin wata hira da kafar yaɗa labarai ta Al-Arabiya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambata.
Ya kuma ce ya yi magana da kwamandan ‘yantawayen, Abu Mohammed al-Jawlani dangane da lokacin miƙa mulkin.
Da safiyar yau ne kafar yaɗa labarai ta Al-Arabiya ta ambato firaministan na cewa bai yi magana da shugaba Bashar al-Assad ba tun ‘jiya da yamma’ kuma bai san inda shugaban ya shiga.
Da safiyar yau ne firaministan ya yi gabatar da jawabi ga ƙasar ta shafinsa na sada zumunta.
Inda a ciki ya ce a shirye yake ya taimaka wajen yin abin da ya dace a ƙasar.