‘Yan tawaye a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo sun ce sun karbe iko da birnin Goma da ke gabashin kasar, amma gwamnati ba ta tabbatar da ikirarin ba.
Mazauna Goma sun wallafa hotuna da bidiyon yadda mayakan M23 ke sinitiri a titunan birnin, bayan dannawar da suka yi Goma tare da cin galaba kan sojojin Congo.
Dubun-dubatar farar hula ne suka tsere daga birnin Goma a jiya Lahadi, zuwa garuruwa makofta.
An dauki sa’o’i ana musayar wuta tsakanin sojojin Congo da ‘yan tawayen, rahotanni sun bayyana cewa titunan birnin mai hada-hadar jama’a sun yi tsit babu motsin kowa.
Wannan na zuwa ne, bayan ministan harkokin wajen Congo, ya zargi Rwanda da kaddamar da yaki a kasarsa ta hanyar tura sojoji iyakar kasar domin taimakawa ‘yan tawayen M23, zargin da Rwanda ta musanta.