Masau tasi a birnin Landan na fama wajen karɓar kuɗin mota da katin banki na kamfanin Visa daga fasinjojinsu.
Direba Tony Vieira ya ce lamarin ya sa yanzu kwastomominsa sai dai su biya kuɗi hannu.
Lamarin zai iya “haiafar da gagarumar matsala”, in ji shi, yana mai cewa ana zuwa wurin da mutane ba su da kuɗin da za su biya.
Wani direban tasin mai suna Tommy Johnson ya ce ya kasa shiga manhajarsa a yau gaba ɗaya, yayin da ya saba karɓar kuɗin ta hanyar kati.
Sai dai ya yi sa’ar samun fasinjojin da ke da kuɗin a hannu. “Amma fa akwai mutanen da na ƙi ɗauka saboda matsalar.”