Masu neman tsayawa takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC a jihar Rivers, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tare da amincewa da marawa duk wanda ya samu nasarar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.
‘Yan takarar a cikin sanarwar da suka fitar a karshen taron da suka yi a Fatakwal a ranar Litinin, sun ce sun yanke shawarar ruguje tsarin siyasarsu, domin ganin duk wanda ya samu tikitin takarar gwamna a jam’iyyar.
Sanarwar mai dauke da sa hannun ’yan takarar gwamna 10 da tsohon kwamishinan sufuri na jihar Rivers, George Tolofari ya karanta a gaban manema labarai.
‘Yan takarar sun amince da cewa su gudanar da shawarwarin nasu cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da kaucewa yin kaurin suna, cin zarafi da jan kunnen sauran masu son a samu tashin hankali.
Wadanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya sune, Prince Tonye Princewill, Dr Dakuku Peterside, Dr Dawari George, Architect Tonye Cole, Engr. Biokpomabo Awara, Hon. Tutar Ojukaye Amachree, Hon. Mina Tender, Hon. Ibinabo Michael West, Sokonte Davies da Cif Francis Ada.