Wata kungiyar siyasa da zamantakewar Yarbawa mai suna Yoruba Ronu Group (YRG), ta gargadi ‘yan siyasa da sauran masu neman shugabanci a Arewa, inda ta ce, za a rika kallon su a matsayin masu shirya makarkashiya da ke son ta’azzara kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Steve Bayode, ya sanya wa hannu, kuma ya bayyanawa manema labarai a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Juma’a, shugaban kungiyar, Prince Diran Iyantan, ya bayyana cewa masu rajin kare hakkin shugaban kasa na Arewa suna neman “domin kara dagula al’amura a kasar, don ƙarin matsaloli fiye da waɗanda ke hannunmu a halin yanzu.”
Iyantan ya bayyana cewa, da gangan jiga-jigan siyasa ke yada rashin hadin kai a matsayin makamin siyasa. Wannan, in ji shi, wani lamari ne mai hatsarin gaske da zai iya haifar da rikici da ba zai karewa a kasar ba.
Ya ce: “Ayyukan irin wannan, a fili, suna nuna munanan kalamai na kasar, kuma suna iya yaudarar kasar a kan tafiya ta tashi daga hanyar zaman lafiya da wadata a yanzu.