fidelitybank

Ƴan takara su rinka sanya mata a matsayin masu dafa musu

Date:

Uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su dauki mata a matsayin abokan takarar su ga ‘yan takarar da za su fafata a zabe a mukamai daban-daban a fadin kasar.

Aisha Buhari ta yi wannan magana ne a daren ranar Asabar, a lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa buda baki a watan Ramadan a fadar gwamnati da ke Abuja.

Aisha ta gayyaci daukacin masu neman shugabancin kasar nan, a dukkan jam’iyyun siyasa, zuwa buda-bakin watan Ramadan.

Wasu ‘yan takarar shugaban kasa, wadanda suka halarci taron, wanda aka gudanar a dakin taro na gidan gwamnatin, Abuja, sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu; Gwamna Dave Umahi na Ebonyi; Gwamna Bala Mohammed na Bauchi; Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, wanda tsohon gwamnan jihar Edo, Farfesa Oserheimen Osunbor ya wakilta.

Sauran manyan baki sun hada da, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i; Ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio; wanda ya taba zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa Cif Barnabas Gemade; Tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, da hamshakin mai da iskar gas, Tein Jack-Rich, sun halarci taron.

vanguard new

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp