Shugaba Muhammadu Buhari, ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar nan a jam’iyyar APC, da su sasanta a tsakaninsu, don amincewa da mutum guda ya wakilci jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe.
Shugaban ya ba su shawarar ne yayin wata ganawa da ya yi da su da daren ranar Asabar a fadarsa da ke Abuja.
Dukkan masu neman takarar sun halarci wannan ganawa, ciki har da jagoran jam’iyyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, wanda a baya-bayan nan ya furta wasu kalamai kan shugaba Buhari da suka tayar da ƙura.
Sai dai yayin wata zantawa da BBC Hausa, mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu, ya musanta wasu rahotanni da wasu kafafen yaɗa labarai ke yaɗawa da ke cewa, shugaban ya goyi bayan kai mulki kudu