fidelitybank

Ƴan ta’adda sun tare a jihar Nasarawa – Gwamna

Date:

Gwamnan jihar Nasarawa, ya bayyana damuwa game da yadda gungun ‘yan fashin daji ke tururuwa zuwa jiharsa, bayan koro su daga maƙwabtan jihohi.

Gwamna Abdullahi Sule ya ce, jami’an tsaro sun lura da ƙaruwar ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Karu, wadda ke da nisan ƙasa da kilomita 30 daga Abuja babban birnin ƙasar.

“Mun lura da tarin ‘yan fashin nan da aka koro daga jihohin Kaduna da Katsina da Neja da Kebbi musamman a yankunan Rugan Juli da Rugan Madaki da ke Ƙaramar Hukumar Karu,” a cewar gwamnan yayin taron manema labarai ranar Asabar.

“Kazalika, mun ga wasu daga cikinsu a ƙananan hukumomin Wamba da Toto.”

Haka nan gwamnan ya ce, sun yi nasarar kama wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga Gidan Yari na Kuje a Abuja bayan mayaƙan Boko Haram sun fasa shi a watan Yuni.

Wasu mazauna yankunan da Gwamna Sule yake magana sun faɗa wa BBC Hausa cewa sun shaida ƙaruwar satar mutane a yankunan nasu.

thisday news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp