Gwamnatin jihar Zamfara ta bayar da tallafin abinci ga wadanda harin ‘yan bindiga suka rutsa da su a kauyen Sakajiki.
Mataimakin Gwamnan Jihar Hassan Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a Unguwar Sarkin Musulmi Junction Railway Kaura Namoda.
Yayin da yake jajanta wa wadanda abin ya shafa, Mataimakin Gwamnan ya bayyana cewa, Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya riga ya dauki dukkan matakan da suka dace don magance matsalar ‘yan fashi da kuma barazanar barnar rayuka da dukiyoyi.
Gusau ya nuna jin dadinsa da irin jajircewa da nuna damuwa da babban hakimin karamar hukumar, Nasiru Altine Yakamata Kaura ya nuna saboda gaggawar mayar da martani da bayar da rahoton faruwar lamarin a kan lokaci ga hukumar da ta dauki matakin gaggawa.


