Yan sanda shida ne aka gurfanar a gaban shari’a a ƙasar Switzerland a kan tuhume-tuhumen aikata kisa ga wani ɗan Najeriya ba da gangan ba shekara biyar da ta wuce.
Mike Ben Peter ya rasu ne bayan an kama shi a birnin Lausanne.
‘Yan sanda sun ce sun yi amfani da tsarin da aka saba amfani da shi wajen kama mutumin da ake zargi da dillancin ƙwaya.
Jami’an tsaron sun tokare shi a ƙasa bayan ya ƙi yarda a bincika shi.
Lauyoyin waɗanda ake ƙara za su tafka muhawarar cewa mutuwar Mike Ben Peter mai yiwuwa ne ta faru sanadin kwantattun cutuka da yake fama da su.
Iyalan mamacin da kuma ƙungiyoyin yaƙi da wariyar launin fata a Switzerland sun kwatanta abin da ya faru da mutuwar George Floyd, wanda ‘yan sanda suka kashe a jihar Minneapolis ta Amurka.