fidelitybank

Ƴan Sandan sun kashe riƙaƙƙen ɗan bindiga a Katsina

Date:

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ta ce, ta daƙile wani hari da aka kai Magamar Jibiya da Ƙaramar Hukumar Jibiya duk a Jihar Katsina tare da kashe wani gawurtaccen ɗan bindiga.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sanda jihar SP Gambo Isah ya fitar, ƴan sandan sun ƙwace bindiga ƙirar AK 47 guda ɗaya da ƙundun harsasai guda huɗu da ke ɗauke da harsasai 90.

Ɗan bindigan da aka kashe sunansa Ibrahim Dangawo wanda ake zargin shi ya kitsa wani hari da aka kai har aka kashe wani tsohon DPO na Jibiya wato DSP Abdulkadir Rano.

A jiya Litinin da misalin huɗu da rabi na yamma ne ƴan bindiga suka rinƙa harbi kan mai uwa da wabi inda suka kai hari kan wani shingen binciken ƴan sanda a Magama a kwanar Hirji a kan hanyar Jibiya.

Bayan musayar wuta da ƴan sandan suka yi da su, a nan ne ƴan sandan suka daƙile harin tare da ƙwace wasu makamansu.

Sanarwar ta ce akasarin yan bindigan da suka tsira daga harin sun tsira da raunin harbin bindiga.

legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...

Gwamnatin Tarayya za ta gina hanyar sufurin jirgin ƙasa a Kano

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta samar da titin...

Abin da ya sa muke ci gaba da tsare Sowore – Ƴansanda

Kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen kai ɗauki na...

INEC za ta bai wa ɗaurarru damar kaɗa ƙuri’a a lokacin zaɓuka

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta ta duba yiwuwar bai...

Mai ya jawo Matan Zamfara su ka yi zanga-zanga

Ɗaruruwan mata ne tsofaffi da masu shawarya suka gudanar...

Aƙalla mutane 24,000 ne suka ɓata saboda Boko Haram a Najeriya

Kungiyar Agaji ta Red Cross ta bayyana cewa aƙalla...

‘Yansanda ku gaggauta sakin Sowore – Obi

Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter...

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu

Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi...
X whatsapp