Rundunar ƴan sanda, sun yi kira ga duk wanda ya san wani mai shirya bidiyon tsokana a intanet ya ɓatawa, su fito su kai rahoto a kan irin halin da suka shiga.
Trinity Guy yana yin bidiyo ta hanyar shirya labari a kan tsokanar mutane don wallafawa a shafukan sada zumunta kuma dubban mutane ne suke bibiyar harkokinsa.
Wasu daga cikin bidiyon da yake shiryawa sukan nuna shi a lokacin da yake roƙon afuwa da magiyar kada a halaka shi, kafin a ji ƙarar tashin wani abu mai kama da bindiga, daidai lokacin da shi kuma zai faɗi magashiyan tamkar wanda aka harbe.
Irin wannan bidiyo dai na tayar da hankalin mutanen da ke kusa, inda sukan yi matuƙar kaɗuwa, wasu ma su ruga da gudu cikin firgici.
“Ina ganin ya kamata a kama mutumin. Ya kamata mutanen da kan shiga fargaba ta dalilin bidiyon Trinity Guy su rika kai rahoton masu irin wannan wasan barkwanci saboda yawancin ayyukansu na da alaƙa da aikata laifi da fasikanci, da kuma mugunta,” in ji kakakin rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, Olumuyiwa Adejobi.
Ya kara da cewa “Wadannan matan na da hujjar yin shari’a sosai a kan mai bidiyon tsokanar.”
Wasu a shafukan intanet sun mayarwa ‘yan sanda martani, suna cewa kamata ya yi rundunar ta yi maganin cin zarafi da rashawar da ta janyo zanga-zangar EndSars ta Najeriya, maimakon ɓugewa da yunƙurin kama masu shirya bidiyon barkwanci don tsokana.


