Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta ce, ta dakile wani hari da aka kai kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar, tare da samun nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama, tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da safiyar Juma’a.
A cewar sanarwar, ‘yan bindigar, wadanda ba su wuce 24 ba, dauke da bindigu kirar AK-47 sun far wa al’ummar garin, inda suka rika harbe-harbe kai-tsaye da misalin karfe 1:00 na safiyar ranar Juma’a tare da yin awon gaba da mutane biyu.
Gambo ya bayyana sunayen mutanen biyu da aka yi garkuwa da su, Alhaji Aminu Wapa da Wada Sale, dukkansu mazauna kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi ta jihar.


