Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce, ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne mai suna Isah Musa, wanda ya bukaci makwabcinsa ya biya Naira miliyan 100 don gudun kada a yi garkuwa da shi tare da ‘ya’yansa.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa ya fitar, wanda ake zargin mai shekaru 30 da haifuwa ya boye tare da hada baki da wani da ake zargi da aikata laifin domin yi wa makwabcinsa barazana.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ranar 31/07/2022 da misalin karfe 8: 00, wani mazaunin kauyen Makadi da ke karamar hukumar Garko ta Jihar Kano ya shigar da kara cewa, an tuntube shi tare da yi masa barazana ta wayar tarho cewa zai biya Naira Miliyan Dari (N100,000,000:00), in ba haka ba, za a yi garkuwa da kansa ko daya daga cikin ‘ya’yansa.
Wancan, sun yi ciniki, daga baya suka zauna a kan Naira Miliyan Biyu (N2,000,000:00).


