Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce, jami’anta sun kama wani dan bindiga mai shekaru 20 da haihuwa dauke da bindigogi kirar AK-47 guda biyu a unguwar Galadimawa da ke karamar hukumar Giwa a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya fitar a ranar Asabar da ta gabata, rundunar ‘Operation Restore Peace’ da ke aiki a kan sahihan bayanan sirri, sun tarwatsa wani kogon masu garkuwa da mutane da ke dajin Galadimawa, bayan sun yi artabu da ‘yan bindigar cikin wata mumunar bindiga.
A cewarsa, wasu ‘yan ta’addan sun garzaya dajin da raunuka daban-daban
Ya ce an kama daya daga cikin wadanda ake zargin Yusuf Monore dan shekara 20 dauke da bindigogi kirar AK 47/49 guda biyu da harsashi guda biyar masu rai 7.62 X 39mm da kuma wayoyin hannu, kuma a yanzu haka ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike.
Sai dai a halin yanzu jami’an na kan bin diddigin wadanda ake zargi da gudu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Yekini Ayoku, ya yabawa irin rawar da jami’an suka nuna tare da bada tabbacin zurfafa hadin kai da hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro a jihar.
Hakazalika, CP ya kuma bukaci ‘yan kasa da mazauna jihar Kaduna masu bin doka da oda da su kasance masu lura a kodayaushe tare da kai rahoto ga jami’an tsaro cikin gaggawa, tare da ba su tabbacin sirrin duk wata hanyar samun bayanai.


