Jami’an ‘yan sanda da ke aiki da Dragon 26 & 29, da ke aikin tsayawa da bincike na yau da kullun, a kan titin Warri/Sapele a jihar Delta, sun kama wani matashi dan shekara 20 da ake zargin dan fashi da makami ne, Aaron Uko.
Haka kuma sun kwato bindiga guda daya dauke da harsashi guda biyu.
An kama wanda ake zargin ne bayan ‘yan sanda sun kama wata motar kasuwanci ta Volkswagen Jetta, PTN 242 TA, dauke da wasu fasinjoji daga Sapele zuwa Warri.
DAILY POST ta samu cewa wanda ake zargin ya boye bindigar a jikinsa kusa da al’aurar sa.


