fidelitybank

Ƴan Sanda sun mayar wa da Matawalle motocinsa

Date:

Dukannin motocin da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta kwace daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle, ta mayar masa a ranar Asabar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar din da ta gabata ta wata tattaunawa ta wayar tarho, inda ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu, ta umurci dukkanin hukumomin tsaron da suka kwashe motocin daga gidajen Matawalle da ke Gusau da Maradun da su dawo da su cikin sa’o’i 48.

A bisa umarnin gwamnatin jihar, jami’an tsaro sun kwashe motocin daga gidajen tsohon gwamnan biyu.

A cewar Abubakar, “Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.” Inji Abubakar.

Ya kuma bada tabbacin cewa an mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya dake Gusau.

Kakakin Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, Suleiman Idris, ya ce tun farko an kwato motoci fiye da 40 daga gidajen tsohon gwamnan biyu.

Ya tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun dauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

naija news legit

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp