fidelitybank

Ƴan Sanda sun harba borkonan Tsohuwa a kan magoya bayan NNPP a Kano

Date:

Wani hargitsi ya tashi da yammacin ranar Laraba, lokacin da dandazon magoya bayan jam’iyyar NNPP suke gudanar da zanga-zanga a jihar Kano, dangane da hukuncin kotun daukaka kara da soke nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ƴan sanda sun tare masu zanga-zangar wadanda suka yi yunkurin zuwa gadar Kofar Nassarawa, bayan sun gudanar da wani taron addu’o’i a filin Kofar Dan’agundi.

Hotuna a kafofin sada zumunta sun nuna yadda aka kona tayoyi a kan titin zuwa Jami’ar Bayero, lamarin da ya kawo tsaiko ga masu ababen hawa.

Haka zalika, an yi jefe-jefe a lokacin hargitsin, ‘yan sanda kuma sun harba hayaki mai sa hawaye.

Bayanai sun ce an kama wasu daga cikin masu zanga-zangar, sannan an ga karin ‘yan sanda a kan titin zuwa gidan gwamna.

Daga bisani dai, kurar ta lafa.

Magoya bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da jam’iyyarsa ta NNPP sun yi kiran gudanar da abin da suka ce “taron addu’o’i” ne don nuna adawarsu ga hukuncin kotun daukaka kara wanda tun farko ya bai wa Nasiru Yusuf Gawuna nasara na jam’iyyar APC.

Kotun wadda ta yi zamanta a ranar Juma’a 17 ga watan Nuwamba, ta yanke hukuncin cewa Abba Kabir Yusuf ba dan jam’iyya ba ne, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.

Sai dai, bayan fitar da kwafin takardar cikakken hukuncin a ranar Laraba, takaddama ta sake barkewa, inda ‘yan jam’iyyar NNPP ke da’awar cewa su ma hukuncin ya ba su nasara a kan abokan kararsu

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp