Rundunar ‘yan sanda, ta ce, ta kama mutum 781, kan laifukan da suka shafi zaɓe a lokacin zaɓukan ƙasar nan.
Babban sifeton ‘yan sandan ƙasar Usman Baba Alkali ne ya bayyana haka ranar Litinin a lokacin da yake ganawa da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasar 36, tare da wasu manyan jami’an ‘yan sandan.
Karanta Wannan: Siyasa na neman wargaza kan ƴan Najeriya – Sarkin Yarbawa
Yayin da yake cikakken bayani game da kamun, Baba Alkali ya ce an aikata laifukan zaɓe 145 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, inda rundunar ta kama mutum 203.
Sai kuma a lokacin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisun dokokin jihohi inda rundunar ta ce an aikata laifuka 304, lamarin da ya sa rundunar ta kama mutum 578.
Babban sifeton ‘yan sandan ya ce rundunar ta shirya ganawa babban sifeton da kwamishinonin ‘yan sanda na jihohin ƙasar da kuma sauran manyan jami’an ‘yan sandan, don tattauna barazanar da tsaron ƙasar ke fuskanta.
Wanda a cewarsa ‘yan siyasa ke ƙoƙarin tayar da hatsaniya a ƙasar bayan zaɓukan ƙasar da suka gabata.
Ya kuma yi Allah wadai da ‘yan siyasar da suke ƙoƙarin tayar da hargitsi ta hanyar tunzura jama’a domin cimma wasu muradunsu.