Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom a ranar Juma’a, sun ceto wasu masu sana’ar kifi 28 daga kasuwar Ishiet, wadanda ‘yan fashin teku suka yi garkuwa da su a tashar ruwa ta Uruan, a karamar hukumar Uruan ta jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olatoye Durosinmi ne ya bayyana hakan a shelkwatar rundunar, Ikot Akpanabia yayin da yake zantawa da manema labarai a Uyo, babban birnin jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa, da zarar ya samu kiran kai harin daga shugaban karamar hukumar Uruan, Iniobong Ekpenyong, ya tara jami’an ruwa zuwa wurin da suka samu nasarar ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a rafi inda aka yi garkuwa da su gaba daya.
Ya bayyana cewa a ko da yaushe ’yan fashin sun nuna kamar masunta ne don aiwatar da munanan ayyukansu kan fasinjojin da ba su ji ba gani.
A cewarsa, “Mutane 28 maza da mata da kuke gani a nan su ne mutanen da jami’an ruwa na ‘yan sanda suka ceto.