Rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto a ranar Lahadin da ta gabata ta ce, jami’an tsaro sun kama mutane 79 da ake zargi da hannu a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
A wata sanarwa da DSP Sanusi Abubakar, kakakin rundunar ‘yan sandan ya rabawa manema labarai a Sokoto, ya ce wadanda aka kama mutane ne da suka karya dokar hana zirga-zirga da kuma wasu laifuka da suka saba wa dokar zabe.
Sanarwar ta kara da cewa, “Dukkan laifukan zaben da aka yi a cikinsu an yi cikakken bincike tare da mika su ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin gurfanar da su gaban kuliya.
“Yayin da wasu da suka saba wa ka’idar penal code ‘yan sanda sun gurfanar da su gaban kotu. Duk da haka, akwai wasu da ake ci gaba da bincike a kansu.”
A halin da ake ciki kuma, an ayyana Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Sokoto.
Aliyu ya doke jam’iyyar PDP ne bayan ya samu kuri’u 453,661.