Wasu ƙarin mutum hudu ne ake zargin ‘yan sandan Kenya sun kashe yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba William Ruto a jiya, wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu sama da 50 a cikin watan da ya gabata, kamar yadda NTV ta ruwaito.
Mutuwar ta faru ne a gundumar Makueni, Nairobi, da Kitengela.
Hukumar kare haƙƙin bil adama ta ƙasar Kenya ta bayar da rahoton cewa, mutum 50 ne suka mutu tun bayan fara zanga-zangar a ranar 18 ga watan Yuni.
Muƙaddashin Sufeto Janar na ‘yan sandan ƙasar Douglas Kanja ya yi gargadin yiwuwar kutsawar masu aikata muggan laifuka a zanga-zangar, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka mayar da martani mai karfi da hayaƙi me sa hawaye da barbi da harsasai.
Mutane da dama a kananan hukumomin Nakuru da Nairobi da Mombasa da Nyeri da kuma Machakos sun jikkata.
Ƙungiyar ‘yan jarida ta Kenya (KUJ) ta yi kira da a gudanar da bincike a kan wani dan sanda da ya harbe wani dan jarida da ke bayar da rahoto kan zanga-zangar a gundumar Nakuru.
Duk da janye dokar ƙrin harajin da shugaba Ruto ya yi, da rage kashe kudade, da kuma rusa majalisar ministocinsa, masu zanga-zangar na ci gaba da nemansa ya yi murabus, bisa la’akari da cin hanci da rashawa da rashin shugabanci na gari.