Ƴan sanda a ƙasar nan, sun sanya jami’an tsaro cikin shirin ko-ta-kwana bayan zanga-zangar da aka yi ranar Alhamis ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da wani ɗan sanda guda.
Ƴan sanda sun yi arangama da masu zanga-zangar waɗanda suka tare tituna tare da lalata wasu ofisoshin gwamnati a wasu yankunan.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta ce jami’an tsaro sun kashe mutane 13 a lokacin da suke ƙoƙarin wargaza masu zanga-zangar.
Ta zargi jami’an ƴansanda da harbin mai uwa da wabi kan masu zanga-zangar. amma sufeto Janar na ƴansandan ƙasar ya musanta wannan zargin.
Dubban mutane ne suka yi gangami a faɗin ƙasar domin nuna adawa da halin matsin rayuwa da ake fama da ita a ƙasar a halin yanzu.