Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kashe ‘yan ta’adda guda biyu tare da kwato bindiga kirar AK47 guda daya, da kuma dabbobin sata 150 daga hannun ‘yan ta’adda.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya shaida wa manema labarai cewa, DPO mai kula da Mallumfashi ne ya tattara jami’an sa bisa ga kiran gaggawa da ya samu.
Ya ce, ‘yan bindigar sun kai hari a yankin Gandu Karfi, inda suka yi awon gaba da mata hudu tare da tafiya da shanu sama da 150.
A cewar sa, DPO din ya jagoranci tawagar ‘yan sanda tare da yi wa ‘yan ta’adda kwanton bauna, inda suka yi nasarar kashe dan bindiga guda daya, sun kwato bindiga kirar AK47 daya, harsashi hudu, shanu 80 da tumaki 70.