fidelitybank

Ƴan Sanda na amfani da ƙarfin wuce ƙima a kan masu zanga-zanga – Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan Adam

Date:

Kungiyar marubuta ta masu rajin kare hakkin ɗan Adam a Najeriya, HURIWA, ta soki ‘yansandan kasar nan kan yadda suke amfani da karfin da ya wuce kima da kuma makamai a kan masu zanga-zangar da ake yi a Najeriya, wadda ta shiga kwana na uku.

A sanarwara da kungiyar ta fitar ta hannun shugabanta Emmanuel Onwubiko, ta ce yadda ‘yansanda ke tunkarar masu zanga-zangar ta lumana a rana ta uku, ko kadan babu kwarewa da nuna mutuntaka, kuma mugun laifi suke aikatawa.

Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ta ce ‘yansandan sun kama mutane da dama da suka taru a babban filin wasa na kasar da ke Abuja,Moshood Abiola Stadium, domin ci gaba da zanga-zangarsu ta lumana a yau Asabar.

Kungiyar ta yi gargadin cewa mummunan matakin da ‘yansandan ke dauka a kan masu zanga-zangar idan ba a ga illarsa ba yanzu to a nan gaba za a gani, abin da zai biyo baya.

Haka kuma ta ce idan ba a fito da ‘yansandan da suka harbi masu zanga-zanga ba an gurfanar da su gaban shari’a, tare da hukunta su kamar yadda doka ta tanada, lamarin zai iya sake janyo zanga-zangar da aka yi ta neman kawo karshen cin zalin da ‘yansanda ke yi wato #ENDSARS.

legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp