Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas, ya bukaci rundunar ‘yan sanda da ta kama tare da gurfanar da dan takarar gwamna na New Nigeria, NNPP, Abba Kabir Yusuf, bisa zarginsa da kawo ‘yan bangar siyasa.
Abbas, ya ce Yusuf ya mayar da gidan kakanninsa ya zama gidan ‘yan banga na siyasa, inda suke tafka muggan kwayoyi da sauran miyagun ayyuka.
“A yanzu haka, mutane da yawa suna ƙaura daga yankin saboda fargabar rashin tabbas saboda ba za su iya rayuwa da ‘yan baranda ɗauke da manyan makamai kuma a kodayaushe suna shan muggan kwayoyi, shi ya sa ‘yan sanda suka yi gaggawar shiga lamarin,” in ji Abdullahi Abbas.
Ya ce, lamarin idan ba a kama shi kan lokaci ba, zai bude wata kofa ta munanan barazanar tsaro ganin zaben 2023 na gabatowa.
Sai dai da yake mayar da martani kan zargin, kakakin dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar NNPP, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce zargin ba shi da tushe balle makama, sai dai shugaban jam’iyyar APC shi ne ake son gabatar da kansa a gaban hukumomin tsaro saboda kalamansa na rashin zaman lafiya da kalaman kiyayya.