Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ta kubutar da mutum 17 da aka yi garkuwa da su a dazukan Gando, da Bagega da kuma dajin Sunke a karamar hukumar Anka da ke jihar
A wata sanarwa da mai magana da rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya sanya wa hannu, ya ce an sace mutanen ne a kauyukan Akawa da Gwashi da Tungar Rogo da kuma Anka, inda aka kai su sansanin ‘yan ta’adda da ke cikin dazukan.
Sanarwa ta ci gaba da cewa “Rundunar ta kubutar da mutanen ne bayan da jami’an tsaron suka samu bayanan da ke cewa wasu gungun ‘yan ta’adda sun kai farmaki wadannan kauyuka tare da sace mutane masu yawa, inda kuma suka tafi da su cikin dazukan Gando, da Bagega da kuma dajin Sunke”
Mutanen dai sun kwashe kusan mako guda a hannun ‘yan fashin dajin kamar yadda sanarwar ta bayyana.
A baya-bayan nan dai Jihar Zamfara na fuskantar karuwar hare-haren ‘yan fashin daji wadanda ke sace mutane domin neman kudin fansa.
Ko a makon da yabata ma dai ‘yan fashin dajin sun yi harbi kan mai uwa-da-wabi ga mutanen da suka je cin kasuwa a Tashar ‘Yar Sahabi cikin yankin Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar , inda suka kashe mutum tara, tare da raunata mutum biyar ciki har da mata da kananan yara.