Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima ya ce, wadannan sauye-sauyen harajin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke kawowa suna son karfafa tsarin kasar ne ta yadda duk ‘yan Najeriya za su amfana da su.
Jaridar Daily Trust ta ruwato cewa Shettima ya fadi hakan ne ranar Asabar a wani taron na wani kwamiti da shugaban kasa ya kafa kan tsare-tsaren kudi da haraji a Abuja.
Kashim Shettima ya ce, sabanin yadda ake yada jita-jita, gwamnati ta kudiri niyyar “kirkirar tsarin gwamnati da zai tabbatar da cin gajiyar tsarin harajin da dukkan ‘yan kasa za su amfana.”
Kashim da ya samu wakilcin mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka Dr Aliyu Modibbo Umar, ya ce gwamnati ba ta da burin tsawwalawa ‘yan Najeriya.
“Burinmu shi ne sake farfado da tsarin haraji a Najeriya yayin da muke neman abokan hulda da za su sanya hannun jaro mai dorewa kuma kasarmu ta zama wadda ake gogawa da ita da fuskar kasuwanci a duniya baki daya,” in ji shi