fidelitybank

Ƴan Najeriya sun nemi shugaban ƙasar Afrika ta Kudu ya kare su daga kai harin ƴan ƙasar

Date:

‘Yan Najeriya mazauna ƙasar Afirka ta Kudu, sun bukaci shugaban kasar, Cyril Ramaphosa da ya kare su da dukiyoyinsu daga hare-haren kyamar baƙin haure.

Al’ummar Najeriya mazauna kasar, sun yi wannan bukata ne a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula da ake yi wa ‘yan kasashen waje a kasar Afirka ta Kudu.

Al’ummar Najeriya karkashin inuwar kungiyar ‘Nigerian Union South Africa’ (NUSA), sun gabatar da bukatar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban NUSA, Mista Collins Mgbo da kuma sakon email daga Pretoria na kasar Afirka ta Kudu.

Ya ce, “Ina kira ga Shugaba Cyril Ramaphosa da ya taimaki al’ummarmu a wannan mawuyacin lokaci domin kada mu sake rasa ‘yan uwanmu a hare-haren kyamar baki.” in ji Mgbo.

Shugaban NUSA ya ce, ‘yan kasashen waje sun kara damuwa lokacin da kungiyar sama da mutane 2,000 suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ma’aikatan bakin haure a wani bangare na “Operation Dudula”.

Dudula, kalmar Zulu wacce ke nufin “kore baya”, ta sami karbuwa a matsayin alamar haɓakar ƙiyayyar baƙi a Afirka ta Kudu, ƙasar da ta ga matakin rashin aikin yi ya ta’azzara kuma talauci ya ƙara tsananta ta hanyar Coronavirus.

“Rundunar ‘Operation Dudula’ ta fito da wasu daruruwan mutane a cibiyar ‘yan ci-rani da ke garin Soweto na kasar Afirka ta Kudu, tare da marasa aikin yi, dauke da makamai da kuma fusata da ‘yan kasashen waje da suka zarga da karbar ayyukansu, suna rera wa ‘yan kasashen waje ku koma gida. A cewar Mgbo.

Ya yi bayanin cewa NUSA ta damu da tsaron lafiyar ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu lokacin da kungiyoyin suka fara cin zarafi ba bisa ka’ida ba tare da lalata kadarori da kasuwanci na ‘yan kasashen waje, musamman ‘yan Najeriya.

“Mun damu saboda a baya zanga-zangar kyamar baki ta haifar da tashin hankali da sace-sacen shagunan ‘yan kasashen waje.

A shekarar 2008, harin da aka kai wa ‘yan kasashen waje ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 62, kuma a shekarar 2015, an kashe ‘yan’uwa ‘yan Afirka bakwai da ba su ji ba ba su gani ba. In ji jaridar Guardian.

nnnnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An yi sulhu da shugabannin ƴan Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta ƙera makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin ƙasarsa shi...

Isra’ila ta buga gangar yaƙi – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce...

Iran ta na cigaba da luguden makami mai Linzami cikin Isra’ila

Ana ci gaba da zaman dar-dar a Isra'ila yayin...

Alhazan Najeriya sun fara dawo wa daga ƙasar Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta sanar da isowar...

Sojoji sun kama ɗan kasar China da zargin kai wa ƴan Boko Haram kayayyaki

Rundunar sojojin ƙasar nan ta kama wani dan kasar...

Isra’ila ta tsokano tsuliyar Dodo – Iran

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce...

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane...

Farashin man fetur ya tashi bayan Isra’ila ta kai wa Iran hari

Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi bayan...

Isra’ila ta kashe manyan Jami’an tsaron Iran su biyar

Wani hari da Isra'ila ta kira ‘Operation Rising Lion’,...
X whatsapp