Mutuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bar cece-kuce ga ƴan Najeriya, tun bayan bayyana rasuwar sa a birnin Landan.
Tuni haka wasu ƴan Najeriya ke ta tofa albarkacin bakinsu dangane da rasuwar Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta.
Tun a makon da ya gabata ne ake ta raɗe-raɗin rasuwarsa.
A mulkin Buhari ne dai aka kulle iyakar Najeriya da hana shigo da Shinkafa da kuma mayar da tsarin kuɗi wanda aka daina karɓar tsofaffin kuɗi da sauran abubuwa da dama.