Shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Ibrahim Lawan, a karshen mako a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ya roki ‘yan Najeriya da su baiwa jam’iyyar APC mai mulki damar sake mulkin kasar nan har zuwa 2023.
Ya yi wannan roko ne a wani taro na gari da Sanata mai wakiltar Kwara ta tsakiya a majalisar dattawan kasar, Dakta Ibrahim Yahaya Oloriegbe ya kira a dakin taro na Banquet Hall daura da gidan gwamnati a Ilorin.
Oloriegbe ya kuma yi amfani da wannan dama wajen bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a karo na biyu.
Tun da farko dai shugaban majalisar dattawan ya kaddamar da ginin wata cibiyar gyara ma’aikatan jinya da ke asibitin kula da masu tabin hankali na tarayya da ke Budo-Egba a karamar hukumar Asa, tare da kaddamar da cibiyar Idi-Isin Community Heatlh Centre da ke Unguwar Okolowo a Ilorin, wanda Oloriegbe ya taimaka.
Lawan, ya ce, jam’iyyar APC mai mulki ta cika alkawuran da ta yi wa ‘yan Najeriya, dalilin da ya sa ya ce, kamata ya yi a sake baiwa jam’iyyar damar ci gaba da rike madafun iko a dukkan matakan mulki fiye da 2023.