Gwamnatin tarayya ta kwashe ‘yan Najeriya 598 yawancinsu dalibai da suka tsere daga kasar Ukraine zuwa kasashe makwabta, sakamakon mamayar da kasar Rasha ta yi musu.
A cewar Daily Trust, sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe dake Abuja a rukuni na biyu a cikin jiragen Max Air da Air Peace.
Yayin da kashin farko na fasinjoji 415 suka isa jirgin Max Air daga Romania, kashi na biyu na fasinjoji 183 sun isa Poland ne da karfe 6:30 na yamma a cikin jirgin Air Peace.
Sun samu tarba daga ministar harkokin jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouk, Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Alh. Mustapha Habib Ahmed da Kwamishinan ’Yan Gudun Hijira na Tarayya, Imam Suleiman Ibrahim.