Gwamnatin Najeriya ta tarɓi ‘yan ƙasar 147 aka kwaso daga maƙwabciyarta Jamhuriyar Nijar, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.
Mutanen da suka ƙunshi maza 129 da mata 17 da jariri ɗaya, sun sauka ne a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas jiya Laraba da misalin ƙarfe 5:20 na yamma.
Nijar ce babbar hanyar da mazauna yammacin Afirka ke yin zango a yunƙurinsu na shiga ƙasashen Libya da Tunisia domin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.
Wannan dalilin kan jawo mutane da dama su maƙale a ƙasar ta yadda sai wasu ƙungiyoin ƙasashen duniya da gwamnatoci sun agaza musu domin komawa gida.